Siffatus Salatin Nabiyyi Jafar 4+
Yadda Sallar Manzon Allah Take
Abdulkarim Nasir
Designed for iPad
-
- USD 1.99
Screenshots
Description
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 & Read - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
Manhajja domin koyon sallah irin ta Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 - Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
Download this app to learn how to pray the Muslim Prayer as taught by Prophet Muhammad (s.a.w). The audio is in Hausa language and works perfectly offline. You can also follow the lessons by reading the sift Salah an-nabi in Arabic text
Siffatus Salatin Nabi mp3 da pdf karatun littafin (Sifat Salat Nabiy Hausa) a inda mawallafin littafin Muhammad Nasiruddeen Al Albani yayi bayanin yadda sallar manzon Allah (s.a.w) take tun daga kabbarar-harama har zuwa sallama kamar kana Kallon Annabi yanayin sallar. Fassarar littafin da darusan na marigayi mallam Jafar Mahmud Adam ne.
Siffatus Salatin Nabiyyi MP3 Offline
Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam
An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tun kafin zuwansu Kano, marigayi Sheikh Ja'afar yariga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan
kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993.
Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan.
Kafin rasuwarsa, ya riga yayi nisa wajen karatunsa na digiri na 3, wato digirin digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano.
Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre).
Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da aka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya bar mata 2, da 'yaya 6, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.
What’s New
Version 1.1
- App now works on iPad and iPhone
- You can now read the Siffatus Salatin Nabiyyi to follow the lessons
- New beautiful user interface. Enjoy!
App Privacy
The developer, Abdulkarim Nasir, has not provided details about its privacy practices and handling of data to Apple. For more information, see the developer’s privacy policy.
No Details Provided
The developer will be required to provide privacy details when they submit their next app update.
Information
- Provider
- Abdulkarim Nasir
- Size
- 159.1 MB
- Category
- Education
- Compatibility
-
- iPhone
- Requires iOS 12.0 or later.
- iPad
- Requires iPadOS 12.0 or later.
- iPod touch
- Requires iOS 12.0 or later.
- Mac
- Requires macOS 11.0 or later and a Mac with Apple M1 chip or later.
- Apple Vision
- Requires visionOS 1.0 or later.
- Languages
-
English
- Age Rating
- 4+
- Copyright
- © 2019 Abdulkarim Nasir
- Price
- USD 1.99
Supports
-
Family Sharing
Up to six family members can use this app with Family Sharing enabled.